Turkiyya : 'Yan adawa sun yi watsi da samakon zabe
April 20, 2017Talla
Hukumar zaben kasar ta Turkiyya ta yi watsi da kiraye-kirayen jam'iyyun adawar kasar na a soke zaben raba gardamar fadada karfin ikon shugaban Raccep Tayyip Erdogan da aka yi a farkon wannan makon, zaben da aka yi zargin kura-kurai a cikinsa.Hakan dai ya haddasa zanga-zanga daga 'yan kasar wadanda suka yi kiran da a rusa majalisar jagororin hukumar zaben kasar, yayin da a daya hannun masu adawar ke tabbatar da cewar za su kai batun gaban babbar kotun kasar.