1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya ta gayaci jakadin Jamus a Ankara

Abdourahamane Hassane
September 18, 2017

Ministan harkokin waje na Turkiyya ya sake gayatar jakadin Jamus a birnin Ankara a karo na biyu a cikin kwanaki uku domin yi masa tambayoyi.

https://p.dw.com/p/2kEG2
Deutscher Diplomat Martin Erdmann
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Carstensen

Wata majiyar diplomasiya ta Turkiyya ta ce jakadin na Jamus Martin Erdmann ya amsa gayatar ce wadda dadewa aka bukaci ya bayyana a ofshin ministan harkokin waje na Turkiyyan. Hukumomin Turkiyyar  sun gayaci jakadin ne a game da wata zanga-zangar da magoya bayan kungiyar Kudawa ta PKK  ta shirya  a Jamus. Wannan dai shi ne karo na 17 da hukumomin Turkiyyar ke gayatar jakadin na Jamus a Ankara.