Turkiyya ta bukaci Jamus ta kama Saleh Muslim
March 5, 2018Talla
Bayan an sakeshi,Saleh Muslim ya isa a kasar Jamus,kuma Turkiyya na zarginsa da hanun a wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota, a shekara ta 2016 a birnin Ankara wanda a ciki mutane 36 suka mutu. Ministan harkokin waje na Turkiyya ya ce zai tattauna batun, a gobe Talata, tare da takwaransa na Jamus Sigmar Gabriel.