Turkiyya ta ayyana zaman makoki | Labarai | DW | 11.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta ayyana zaman makoki

Wani harin ta'addanci da aka kai a Turkiyya ya yi sanadiyyar rayukan 'yan sanda 30 da fararen hula bakwai da kuma raunata sama da mutane 150.

Turkiyya ta ayyana zaman makokin ne yayin da aka kaddamar da bincike da fara aikin binne wadanda suka rasa rayukansu sakamakon tagwayen hare-hare da suka yi sanadi na rayukan mutane 38 da raunata wasu 155 a kusa da filin wasa na birnin Santanbul.

Harin kunar bakin waken da aka kai a motoci biyu a daren Asabar din da ta gabata, an kai shi ne a kusa da filin wasan kungiyar kwallon kafa ta Besiktas wanda hakan ya tada hankulan mahukunta ciki har da Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya sha alwashi na zakulo wadanda ke da hannu a harin, da ya bayyana da zama babbar barazana ga tsaron al'ummar kasar.

Harin dai ya yi sanadi na rayukan 'yan sanda 30 da fararen hula bakwai da wani da ba a fayyace ba, kamar yadda ministan harkokin cikin gidan Turkiya Suleyman Soylu ya shaidawa 'yan jarida. Tuni dai aka cafke wasu mutane 13 da ake zargi da hannu wajen kitsa harin.