1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya na shirin kai farmaki cikin Iraqi, a misalin Isra'ila a Lebanon.

YAHAYA AHMEDJuly 21, 2006

Rahotanni na nuna cewa kusan dakaru dubu ɗari da 50 ne Turkiyya ke shirin turawa zuwa arewacin Iraqi, don fatattakar ƙungiyar PKK ta kurdawa, ta bin misalin kutsawar da Isra'ila ta yi a ƙasar Lebanon don yaƙan ƙungiyar Hizbullahi, da uzurin cewa tana kare kanta ne.

https://p.dw.com/p/Btyw
Zanga-zangar Kurdawa a kudu maso gabashin Turkiyya.
Zanga-zangar Kurdawa a kudu maso gabashin Turkiyya.Hoto: AP

A jihohin kudu maso gabashin Turkiyya, kusan kullm sai an yi jana’izar sojojin da bamabaman ƙarƙashin ƙasa suka halaka. An dai daɗe ana fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin Turkiyyan da mayaƙan ƙungiyar ta PKK a yankunan gabashin ƙasar. Ban da dai sojojin, a wasu lokutan bamabaman ƙarƙashin ƙasar na tashi su halakad da faraen hula, a galibi mata da yara. ’Yan ƙungiyar PKKn dai na yaƙin gwagwarmaya ne don samo wa kansu ’yanci, saboda abin da suke gani kamar danniyar da ƙasar Turkiyyan ke yi musu.

A nata ɓangaren gwamnatin Turkiyya na ɗaukan Kurdawan ne tamkar ’yan ta’adda. Tana kuma zargin ƙasashen Yamma da rashin ɗaukar asarar rayukan da fararen hular ƙasar ke yi a wannan gwagwarmayar da Kurdawan, da muhimmanci. Kamar dai yadda Firamiyan ƙasar Tayyip Erdogan ya bayyanar:-

„Mafi yawansu na auna ababan da ke wakana a Isra’ila ne da mizani ɗaya, sa’annan ayyukan ta’addancin da ake gudanarwa a Tukiyya kuma da wani mizanin daban. To amma ai bai dace a kalli ta’addanci a Turkiyya da mizani daban da na Gabas Ta Tsakiya, ko Afghanistan, ko Somaliya ko Madrid ba. Ta’addanci, ko ina ya auku a duniya, ta’addanci ne.“

Firamiyan Turkiyyan dai na bayyana ɓacin ransa ne da farko ga Amirka, wanda yake gani kamar tana da hannu a asarar rayukan da fararen hulan Turkiyyan ke yi a wannan gwagwarmayar da Kurdawa. Mahukuntan Turkiyyan, sun yi imanin cewa, daga arewacin Iraqi ne Kurdawan ke shirya maƙarƙashiyarsu, kafin su kuɗaɗo cikin Turkiyyan don gudanad da ɗanyen aikinsu na abin da suke kira ta’adanci. A yankin arewacin Iraqin kuwa, su Amirkawan ne ke da angizo. Tun da ’yan tawayen Kurdawan suka janye daga Turkiyan a shekaru 7 da suka wuce, sun kafa sansanoninsu ne a cikin tsaunukan Kandil da ke arewacin Iraqin. A nan ne kuma, suke iya samun duk makamai da bamabaman da suke bukata, sa’annan daga nan ne kuma suke kutsawa cikin Turkiyyan don kai hare-hare. In an biyo su kuma su tsere su dawo cikin Iraqin. Idan ko sun tsallake iyakar da ke tsakaninsu, Turkawan ba za su iya biyo su cikin Iraqin ba, saboda Amirka ta hana musu yin haka.

Tun ’yan shekarun da suka wuce ne dai, mahukuntan birnin Ankara ke ta neman alfarma daga Amirkan, wato da ta fattataki mayaƙan Kurdawan da kanta, ko kuwa ta ba su izinin tura dakarunsu su kammala wannan aikin. Amma har ila yau Amirka ba ta amince da wannan bukatar ba. Bisa dukkan alamu dai, gwamnatin birnin Ankaran ta gaji da romon bakan da Amirka ta sha yi mata. A halin yanzu da ta ga Washington ta ƙyale Isra’ila tana cin karenta babu babbaka a Lebanon, tana kuma yaƙan ƙungiyar Hizbullahi, ita ma tana ganin lokacinta ya zo da za ta yi katsalandan a arewacin Iraqin don fatattakar ’yan ƙungiyar PKKn, da uzurin cewa tana kare kanta ne, kamar dai yadda Isra’ila ma tace tana da ’yancin kare kanta da kai farmaki a Lebanon.

’Yan ƙasar Turkiyyan da dama na nuna ɓacin ransu ga magana da baki byiu-biyu da Amirka ke yi, inda a ɓangare ɗaya take amanna da ɗaukin da Isra’ila ke yi a Lebanon, amma a ɗaya ɓangaren, take hana Turkiyyan kutsawa cikin arewacin Iraqi. A ƙarshen makon da ya gabata ma, sojojin Turkiyya 14 ne suka rasa rayukansu, a wani kwanton ɓaunar da ’yan ƙungiyar PKKn suka yi musu a gabashin ƙasar.

Rahotanni dai sun ce Turkiyya ta fara tura rukunan sojinta zuwa yankin iyakarta da Iraqin, da shirin kai farmaki ga guraban Kuradawan a cikin tsaunukan arewacin Iraqin. Kafofin yaɗa labarai sun ari bakin jakadan Iran a birnin Ankara yana mai cewar ƙasarsa za ta goyi bayan wannan matakin. Kai tsaye ne dai jakadan Amirka a Turkiyyan, shi ma ya gargaɗi mahukuntan ƙasar da su guji ɗaukan irin wannan matakin musamman tare da haɗin gwiwar Iran.

Amma bisa dukkan alamu, Turkiyya na watsi da wannan gargaɗin. Bisa cewar Firamiyan ƙasar Tayyip Erdogan dai:-

„Ba jakadan Amirka ne zai yanke mana shawara kan matakin da za mu iya ɗauka ko mu bari ba. Wannan shawarar ta rataya ne kacokan a wuyar gwamnatin Jumhuriyar Turkiyya. Mu da kanmu ne za mu yanke wa kanmu shawara kan abin da za mu yi. Kuma mu da kanmu ne za mu ɗau matakan da muka ga sun fi dace mana.“