Turkiyya na shirin afkawa kurdawan Iraqi | Labarai | DW | 10.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya na shirin afkawa kurdawan Iraqi

Kasar Turkiyya ta girke dakarun sojin ta zambar dubu dari da 40 a iyakar kasar da Iraqi. A cewar ministan harkokin Iraqi, Hosher Zubari, Turkiyyan ta jibge sojin nata ne a arewa da iyakar kasar ta Iraqi.Mr Zuberi , ya kara da cewa a dai dai lokacin da ake kokarin samo bakin zaren tabbatar da zaman lafiya a kasar, a dai dai lokacin ne sojin na Turkiyya ke jiran umarnin afkawa tsageru kabilar kurdawa dake yankin. Duk da cewa fadar White House ta Amurka na da tunanin ganin an dauki mataki irin na Turkiyya kann Kurdawan, tuni ta bukaci mahukuntan na Turkiyya da kada su yaki kurdawan. Yin hakan a cewar Fadar ta White House, abu ne daka iya rura wutar rikice rikice da tashe tashen hankula a kasar.