Turkiyya na ganawa da ƙungiyar EU. | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya na ganawa da ƙungiyar EU.

Ƙasar Turkiyya ta fara shawarwari yau da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai game da batun neman shigarta cikin ƙungiyar. Wannan ganawar dai ta zo ne bayan Turkiyyan ta bayyana matuƙar ɓacin ranta game da wata dokar da majalisar Faransa ta zartar, wadda ke haramta duk wani yunƙurin ƙaryata kisan gillan da aika yi wa Armeniyawa a lokacin mulkin daular Usmaniyya na Turkiyyan a cikin shekara ta 1915.

Ita dai ƙungiyar EU na neman Turkiyyan ta buɗe tashoshin jiragen ruwanta ne ga ƙasar Cyprus, wadda tuni take cikin ƙungiyar Haɗin Kan Turan.