1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Mutane 4 sun mutu a harin bindiga

Ramatu Garba Baba MNA
April 5, 2018

Wani dan bindiga ya bude wuta kan abokan aikinsa inda ya harbe mutane hudu har lahira a wata jami'a da ke yankin Anatolia a tsakiyar kasar Turkiyya.

https://p.dw.com/p/2vXpd
Türkei Polizist in Istanbul
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Akgul

Wata kafar yada labaran kasar Turkiyya mai suna Dogan ta ce 'yan sanda sun yi nasarar cafke dan bindigan bayan da ya kai harin da ya raunata mutum uku baya ga wadanda suka rasa rayukansu.

Mutumin ya kasance daya daga cikin ma'aikatan jami'ar, amman kuma babu karin bayani kan dalilansa na harbe abokan aikin na sa inji jaridar.

Kawo yanzu ma'aikatar tsaron kasar ba ta iya tantance ko harin na da alaka da ayyukan ta'addanci ba, sai dai ana ci gaba da gudanar da binciken mutumin.