Turkiyya: Binciken harin ta'addanci a Ankara
February 18, 2016Talla
Akalla mutane 28 aka kashe a birnin Ankara na kasar Turkiyya lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta yi bindiga lokacin da motocin bas na sojoji ke jiran denja ta ba su hanya a tsakiyar babban birnin kasar ta Turkiyya.
Ofishin gwamnan birnin ya ce an kai harin ne kusa da gine-ginen gwamnati da shalkwatar soji. Mukaddashin Firaminista Bekir Bozdag ya ce hari ne na ta'addanci.
A kuma halin da ake ciki Firaminista Ahmet Davutoglu ya soke tafiyar da so yi zuwa birnin Brussels. A wasu tagwayen hare-hare da aka kai birnin cikin watan Oktoban 2015 fiye da mutane 100 suka hallaka.