1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta yi fatali tallafin EU

Yusuf BalaOctober 17, 2015

Karkashin yarjejeniyar da suka cimma, kasar Turkiya za ta dauki alhaki na dakile ayyukan dillalai masu fasakaurin bisa tallafin kudi da za ta samu daga kasashen na EU.

https://p.dw.com/p/1GpmS
Türkei PK Außenminister Feridun Sinirlioglu Drohnenabschuß
Feridun Sinirlioglu ministan harkokin wajen TurkiyaHoto: Reuters/U. Bektas

A wani labarin kuma kasar Turkiya ta yi fatali da tayin tallafin kudi da kungiyar kasashen Turai ta yi mata dan rage radadin kalubalen kwarar 'yan gudun hijira.

A wani taro da suka gudanar cikin makon nan a birnin Brussels, mambobi daga kasashen na EU sun cimma matsaya kan dabarun da za su bi wajen ganin sun tsaida dubban 'yan gudun hijirar da ke kwarara zuwa kasashensu.

Karkashin yarjejeniyar da suka cimma kasar Turkiya za ta dauki alhaki na dakile ayyukan dillalai masu fasakaurin bisa tallafin kudi da za ta samu daga kasashen na EU, sannan al'ummar ta Turkiya su rika samun takardar Visar shige da fice tsakanin kasashen na EU cikin sauki. Ministan harkokin wajen kasar ta Turkiya Feridun Sinirlioglu ya jaddada cewa har yanzu ba a kammala yarjejeniya ba da kasashen na EU kuma kudaden da kasashen na EU suka yi tayin bada su a matsayin tallafi ba za a amince da su ba.