1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan tura sojojin Turkiya zuwa Iraki

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 5, 2015

Iraki ta ce jibge sojojin Turkiya a kusa da birnin Mosul na kasar ya sabawa dokokin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1HHvv
Fouad Massoum shugaban kasar Iraki
Fouad Massoum shugaban kasar IrakiHoto: picture alliance/AP Photo

Shugaban kasar Iraki Fouad Massoum ya bukaci kasar Turkiya da ta janye daruruwan sojojinta da ke kusa da arewacin birnin Mosul. Massoum ya bayyana jibge sojojin na Turkiya a kasarsa da cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa kana zai iya iza wutar rikici a yankin. A wata sanarwa da aka yada ta kafar sadarwa ta Internet, Massoum ya bukaci ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Irakin da ta yi duk mai yiwuwa wajen kare kan iyakokin kasar da kuma tabbatar da cikakken 'yancin da Irakin ke da shi. Wata majiyar tsaron kasar Turkiyan ta sanar da cewa Ankara ta tura daruruwan sojojinta zuwa Irakin ne domin bai wa sojojin kasar horo a kusa da birnin na Mosul.