Turkiya ta saki dan jaridar nan Bajamushe
February 16, 2018Talla
Gidan jaridar da yake aiki a Jamus Die Welt, ya bayyana sakin dan jaridar a shafinsa na Twitter a wannan rana ta Jumma'a inda ya bayyana samun wannan bayanai daga lauyan da ke kare dan jaridar. Ya ce an saki dan jaridar Yücel mai shekaru 44 bayan tsare shi ba tare da yi masa shari'a ba, lamarin da ya kara rura wutar rikici tsakanin mahukuntan Berlin da Ankara da ke zama kawayen juna a kungiyar tsaro ta NATO.
Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya fada wa manema labarai a birnin Munich cewa suna cike da fata na ganin dan jaridar nan ba da dadewa ba ya bar kasar ta Turkiya.