Turkiya ta sake kai hari kan ´yan PKK a arewacin Iraqi | Labarai | DW | 22.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta sake kai hari kan ´yan PKK a arewacin Iraqi

Wata majiyar tsaro ta Kudawan Iraqi ta tabbatar da cewa jiragen saman yakin Turkiya sun sake kai hare hare a arewacin Iraqi inda suka farma wasu ƙauyukan Ƙurdawa. Jabbar Yawar kakakin dakarun tsaron Ƙurdawan Iraqi ya ce dazu da rana jiragen saman yakin Turkiya suka kai wannan farmaki. Ya ce ba su san yawan barnar da suka yi ba, to amma rundunar Turkiya ta ce a harin wanda ta kai akan ´yan tawayen kungiyar PKK, ta halaka ɗaruruwan mayakan kungiyar ta PKK. Rundunar ta ce a farkon mako mai zuwa zata buga hotunan wannan hari da ta kai. Rikici tsakanin PKK da sojojij Turkiya ya taɓarɓare ne bayan da PKK ta kashe sojoji a ɓangaren Turkiya na kan iyakarta da Iraqi.