Turkiya ta lashi takobin daukar mataki kan Qurdawa | Labarai | DW | 22.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta lashi takobin daukar mataki kan Qurdawa

Kasar Turkiya ta lashi takobin daukar tsatsauran mataki kann yan tawaye Qurdawa da suka kashe sojojinta 17.wannan hari mafi muni daga yan tawayn PKKtun fiye da shekaru 10 ya faru ne kwanaki hudu bayan majalisar dokokin Turkiya ta amince da tura dakarun kasar domin su yaki yan tawaye a arewacin Iraki.

A halinda ake ciki dai firaminsita Racib Tayyib Erdogan yace bayan tattaunawarsa da sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice,ta bukaci shi da ya dakata kafin maida martani kann yan tawayen.Turkiya ta aike da sojoji kusan 10,000 da kayan yaki zuwa bakin iyaka kasar da Iraki.wata sanarwa kuma daga shugaba Abdullahi Gul ta baiyana cewa Turkiya zata yi iyaka kokarinta wajen ganin an kawo karshen taadanci.