1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta katse dangantaka da kasar Holland

Yusuf Bala Nayaya
March 14, 2017

Dukkanin kasashen dai na Jamus da Holland sun hana ministoci na kasar Turkiya gudanar da gangamin tallata Shugaba Erdogan.

https://p.dw.com/p/2Z7cq
Recep Tayyip Erdogan und Mark Rutte
Hoto: picture alliance/dpa/M.Beekman

A ranar Litinin kasar Turkiya ta katse dangantaka da kasar Holland da ma tsayar da komawar jakadansu bayan da dangantaka ke kara dagulewa tsakanin kasashen a ta dalilin hana jami'an gwamnatin Turkiya gudanar da tarukansu a kasar ta Holland.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan dai ya zargi Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da "tallafar 'yan ta'adda" bayan da take kara wari tsakanin kasar ta Turkiya da kasashen na Turai, abin da ake ganin  ka iya sanin lalacewar dangantakar Turkiya da sauran kasashen na Turai.

Dukkanin kasashen dai na Jamus da Holland sun hana ministoci na kasar Turkiya gudanar da gangami irin na siyasa, gangamin da ke zama na tallata muradun Shugaba Erdogan na neman karin karfin iko a kuri'ar raba gardama da za a yi a ranar 16 ga watan Afrilu.