Turkiya ta ja kunnen Kungiyar EU kan mutunta yarjejeniya | Labarai | DW | 07.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta ja kunnen Kungiyar EU kan mutunta yarjejeniya

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya gargadi kungiyar EU da cewar ba za su mutunta yarjejeniyar da suka cimma da Kungiyar EU ba kan dakile kwararar 'yan gudun hijira

.Shugaban Turkiyan a yayin wani jawabi gaban wani taro a Ankara yayi nuni da cewar.

''Akwai ka'idoji ko hanyoyin da yakamata abi kuma a kwai wasu sharuda,idan dai kungiyar EU ta kasa daukar matakan da yakamata ta dauka ko ta gaza cika dukkanin alkawarurrukan da ta yi,to Turkiya ma ba za ta martaba yarjejeniyar ba.''

Tun dai a watan Maris ne aka cimma yarjejeniyar tare da zayyana matakan da za a bi wajen dakile kwararar 'yan gudun hijira zuwa Kasashen Turai a inda Turkiya ta amince da karbar 'yan gudun hijirar da suka futo daga kasar Girka abisa sharadin samun tallafin Euro Biliyan 6 daga hannun Kungiyar.