1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya ta ce ba a yi mata adalci a tattaunawar dsaukar ta cikin EU

December 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuYD
FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi watsi da shawarar da ministocin harkokin waje na KTT suka yanke ta dakatar da tattaunawar daukar Turkiya cikin kungiyar da cewa ba´a yi adalci ba. Erdogan ya ce kungiyar EU ba zata iya warware rikicin dake tsakanin Turkiya da Cyprus ba saboda haka ya kamata MDD ta tsoma baki. A kuma halin da ake ciki wani jigo na jam´iyar dake jan ragamar mulki a Turkiya, Koksal Toptan ya ce shawarar da EU din ta yanke ba zata sa gwamnati a birnin Ankara ta yi fatali da shirinta na samun wakilci a cikin kungiyar ba. A makon jiya Turkiya ta yi tayin bude tashoshin ta biyu na jiragen ruwa ga yankin Girika na tsibirin Cyprus bisa sharadin cewa za´a dage takunkuma cinikaiya da aka dorawa yankin Turkiya din a Cyprus.