Turkiya ta cafke jagoran Kungiyar Amnesty
June 7, 2017Jagoran Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International a Turkiya, ya zo hannun mahukunta bisa zargin alaka da fitaccen malamin nan Fethullah Gulen, da mahukuntan Ankara ke zargi da zama kanwa uwar gami a kitsa juyin mulki da ya gaza nasara a kasar a shekarar bara.'Yan sanda dai sun cafke lauyan Taner Kiliç tare da wasu 22 a Yammacin birnin Izmir duk dai bisa zargin alaka da malamin da ke zaune a Amirka kamar yadda Kungiyar Amnesty ta wallafa a shafinta na intanet.
A cewar sakatare janar na kungiyar ta Amnesty Salil Shetty, ya kamata mahukuntan na Turkiya su gaggauta sakin Kiliç da wasu lauyoyin 22 da aka kama a kuma yi watsi da duk wasu zarge-zarge marasa tushe da ake musu.
Taner Kiliç ya yi fice wajen caccakar mahkuntan na Ankara kan rashin mutunta 'yanci na fadin albarkacin baki a cewar Shetty. Sama da mutane 100,000 ne dai aka kora daga aiki ko aka dakatar da su bisa zargin hannu a juyin mulkin da ya gaza nasara a Turkiya a bara.