Turkiya ta buƙaci Iraƙi da ta rufe sansanonin ´yan tawayen ƙungiyar PKK | Labarai | DW | 20.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta buƙaci Iraƙi da ta rufe sansanonin ´yan tawayen ƙungiyar PKK

FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayi kira ga gwamnatin Iraqi da ta rufe sansanonin da ´yan tawayen Kurdawa ke amfanin da su dake arewacin Iraqin. Hakazalika gwamnati a birnin Ankara ta nemi takwararta a Bagadaza da ta mika mata shugabannin kungiyar Kurdawa ta PKK. A ranar laraba da ta gabata majalisar dokokin Turkiya ta bawa dakarun kasar ikon yin kutse cikin arewacin Iraqi don farautar ´yan tawaye wadanda ke amfani da wannan yanki suna kaddamar da hare hare a cikin Turkiya. Gwamnatocin biranen Bagadaza da Washington sun yi kira ga Turkiya da ta guji daukar matakan soji suna masu cewa hakan zai haddasa rudani a yankin baki daya.