1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na fuskantar matsaloli wajen dakile yaduwar murar tsuntsaye

January 8, 2006
https://p.dw.com/p/BvDA

Wasu ´yan Turkiya su biyar ciki har da kananan yara maza 2 sun kamu da nau´in H5N1 mai kisa na cutar murar tsuntsaye a daidai lokacin da kwayoyin cutar ke ci-gaba da bazuwa a yammacin kasar zuwa nahiyar Turai. A halin da ake ciki hukumomin Turkiya na fuskantar matsaloli ta yadda zasu dakile yaduwar kwayoyin cutar. A halin da ake ciki wata tawagar kungiyar lafiya ta duniya WHO ta tashi zuwa yankunan da cutar suka bulla a gabashin Turkiya, don kimanta irin martanin da gwamnati ta mayar tare da duba yiwuwar ko kwayoyin zasu iya bazuwa tsakanin ´yan Adam. Wani jami´in ma´aikatar kiwon lafiya ya fadawa kamfanin dillancin labarun kasar cewa mutane biyu a birnin Van dake gabashin kasar da kuma sauran 3 a birnin Ankara sun kamu da kwayoyin nau´in H5N1. Yanzu haka dai yawan wadanda suka kamu da kwayoyin cutar mai kisa sun kai mutum 9 dukkansu yara kanana, in banda mutum daya.