Turkiya da Siriya suna ƙarfafa hulɗa tsakaninsu | Siyasa | DW | 23.12.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turkiya da Siriya suna ƙarfafa hulɗa tsakaninsu

Dangantakar haɓaka tattalin arziki tsakanin Damaskus da Ankara sai ƙara bunƙasa take yi

default

Bashar Assad da Recep Tayyip Erdogan a fadar Ash-Shaeb Damaskus, Siriya,

Firayim ministan ƙasar Turkiya RacepTayyip Erdogan ya kai wata ziyara a ƙasar Siriya, wannan ziyarar za ta ƙarfafa hulɗar dangantaka tsakanin ƙasahen biyu. wanda za ta haɗa da tattalin azriki da siyasa.

Shugaban ƙasar Siriya Bashar Al'assad ya na kai kawo domin dawo da martabar ƙasar a siyasar duniya, bayan da ta yi shekaru 29 ana maida ita saniyar ware a ƙarƙashin shugabancin babansa. Abinda ya sa Siriya ba ta da abokanan hulɗa na ƙud da ƙud masu yawa.

Bayan kisan da akayiwa tsohon shugaba Saddam Husaini, dangantakar Damaskus da Bagadaza ta ɗan fara farfaɗowa sannu a hankali. Haka ma Siriya ta samu kanta cikin wata rigima, bayan mutuwar tsohon firayim ministan ƙasar Lebanon Rafiƙ Hariri, inda ƙasashen yamma suka ce Siriya na da hannu, abinda ya tilastawa sojojin ta janyewa daga ƙasar ta Lebanon. Amma dai an ci gaba da ɗaukar matakan dipalamasiya tsakanin ƙasashen biyu. Batun ɗasawar da Siriya keyi da Iran, shi ma ya na da ga cikin abin da ke sa ƙasashen yamma ba sa sakarma Damaskus mara, sabo da maida Tehran saniyar ware a duniya.

Shugaba Assad ya bi ta hannun shugaban ƙasar Faransa Nicolaz Sarkozy, wajen samun sassauci da ga ƙasashen Tarrayar Turai, to amma wanna bai haifara da wani ɗa mai ido ba i zuwa yanzu. Gwamnati shugaban ƙasar Amirka Barack Obama, ta yi alƙawarin maida hulɗar dangantaka da Siriyara, wanda aka yanke tun shekara ta 2005, amma har yanzu babu alamar samun hakan.

Wannan ziyarar da Firimiya Racep Tayyip Erdogan ya kai Siriya, wata alamace ta ƙara samun nassara ga ƙasar ta Siriya. Siriya da Turkiya su na ta ƙara kusantar juna ta fanni haɓaka tattalin arziki da wassu fannonin masu yawa. Haka kuma ita ma Turkiya yanzu ta na ƙara mai da hankalinta kan ƙasashen larabawa, ba kamar yadda ada ta yi watsi da su, ta ɗora koɗoyinta kan shiga ƙungiyar tarayyar Turai kawai.

A zamanin mulkin ɗaular Usumaniyya, ƙasar Siriya ta kasance ɗaya daga ƙasashen da ke ƙarƙashin ɗaular, kafin Faransa ta mamaye ƙasar. Yanzu ƙasashen Turkiya da Siriya, su na son mantawa da bayan domin gina gaba.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Peter Philipp

Edita: Ahmad Tijani Lawal