Shugabanin kungiyar Turai sun bukaci daukar kwararan matakai domin magance yamutsin kasar Burundi bayan mutuwar mutane da yawa a sakamakon harin da aka kai kan wani barikin sojojin kasar.
Kimanin mutane 87 suka mutu a kasar ta Burundi bayan wasu hare-hare da 'yan tada kayar baya suka kai a kan wani barikin sojoji a ranar Jumma'a wadanda ake kyautata zaton masu adawa da tazarcen Shugaba Pierre Nkurunziza ne.
A yayin taron ministocin kasashen Turan da suke gudanarwa a birnin Brussels, kantomar harkokin wajen EU Federica Mogherini ta yi nuni da cewar:
Sun tuntubi shugabanin kungiyar Afrika da su shiga a dama da su wajen tattauna batun zaman lafiyar Burundi bisa jagorancin yankin.