1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai: Diesel zai kashe mutane 5000

Gazali Abdou Tasawa
September 18, 2017

Wani rahoton bincike da aka wallafa a wannan Litinin ya nunar da cewa a Turai mutane sama da 5000 za su mutu a kowace shekara a sakamakon shakar gurbataccen hayakin injinan Diesel.

https://p.dw.com/p/2k9su
Symbolbild Dieselskandal Automobilindustrie
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Schmidt

Wani rahoton bincike da aka wallafa a wannan Litinin kan illar da hayakin motoci masu dauke da injinan Diesel na boge da Kamfanin Wolkswagen ya sayar a Turai, ya nunar da cewa mutane kimanin dubu biyar ne ka iya mutuwa a kowace shekara a sakamakon shakar gurbataccen hayakin da wadannan motoci suka fitar. Binciken wanda wasu kwararru a fannin muhalli daga kasashen Turai da kuma Amirka suka gudanar ya shafi kasashe 28 na Kungiyar EU da kuma kasashen Norway da Switzerland, ya tabbatar da sahihancin alkalumman binciken farko da aka gudanar jim kadan bayan bankado badakalar kamfanin na Volkswagen a shekara ta 2015 inda kamfanin ya amince da yin ha'inci ta hanyar dora wa injinan motocin nasa wata na'ura da ke boye gaskiyar yawan gurbataccen hayakin da suke fitarwa. Rahoton binciken ya bayyana cewa yanzu haka dai akwai motocin Diesel sama da miliyan 100 da ke aiki a cikin kasashen na Turai.