1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai da Iran na dinke barakar Amirka

Yusuf Bala Nayaya
May 15, 2018

A wannan rana ta Talata ce ministan harkokin wajen Iran zai tattauna da takwarorinsa na Jamus da Faransa da Birtaniya a birnin Brussels na Beljiyam kan yarjejeniyar nukiliya da Amirka ta fita.

https://p.dw.com/p/2xjDc
Symbolbild Kündigung Atomabkommen mit Iran durch USA
Hoto: Imago/Ralph Peters

Wannan tattaunawa na zuwa ne bayan kammalawa da ziyararsa a China da Rasha inda suke tattaunawa kan inda aka kwana game da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran da suka cimma a watan Yuli na shekarar 2015, matakin da ya sa kasar ta tsayar da aikace-aikacenta kan makamashin nukiliya, yayin da a bangaren na kasashen Yamma suka sassauta takunkuman da suka maka wa Iran. Sai dai a makon jiya Amirka bisa jagorancin Donald Trump ta janye hannu daga cikin yarjejeniyar da ma barazanar karin takunkumai ga Iran din.

Kasashen Turai dai sun nunar da cewa suna nan daram kan alkawarin da suka dauka kan shirin yarjejeniyar da Iran, lamarin da a ke ganin zai kara kusanci tsakanin kasashen na Turai da China da Rasha bayan da Amirka ta yi baki biyu.