Turai da Amurika na maida martani ga kalamomin Ahmadu Nidjad | Labarai | DW | 12.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turai da Amurika na maida martani ga kalamomin Ahmadu Nidjad

Ƙasashen Turai da Amurika, sun maida martani ga kalamomin da shugaban ƙasar Iran, Mahamud Ahmadinijad, yayi jiya, inda ƙarara, ya bayyana cewar, tuni, har sun kamalla matakin farko, na sarrapa Uranium, da burin samar da makamashin Nuklea.

Idan dai ba a manta ba, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya ba hukumomin Teheran, wa´adin ranar 28,ga watan da mu ke ciki, domin wasti da wannan shiri, ya kuma umurci hukumar yaƙi da makaman nuklea, da ta gudanar da bincike, domin tabbatar da hukumomin, Iran sun bi wannan umurni.

Gobe ne, bisa yadda a ka tsara shugaban hukumar AIEA, Mohamed El Baradei, zai gana da magabatan Iran, a game da batun.

Mohamed El Baradei, ya ce ba shi yi mamaki ba,ko kaɗan da sanarwar shugaba Ahmadinejad.

Shima Shugaban bataliyar sojojin Iran, a wata hira da manema labarai a yau, ya jaddada cewar barazanar ƙasashen turai da Amurika, ba zata karya lakadarin Iran ba, a game da burin ta, na sarafa makamashin nuklea, domin ƙarfafa wutar lantarki.

Kazalika ya ce, Iran a shire ta ke, ta fuskanci hari, daga ko wane fanni.

A cen Kasar France, kakakin gwamnati, Jean Francois Cope, ya yi Alllah wadai, da sanarwar, ta hukumomi Iran, da ya dangata da matakin tsokanar faɗa.