1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Afrika a Somalia

Zainab A MohammadAugust 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5t

Rahotanni daga kasar kenya na nuni dacewa nanda yan makonni ko kuma watanni ,dakarun kiyaye zaman lafiya na hadin gwiwa da Afrika zasu isa Somalia,akarshin shirin da kungiyar kotunan islama tayi adawa dashi ,kungiyar da kuma ke barazana wa gwamnatin rikon kwarya a somalia.A hannu guda kuma kungiyar musulmin sun dada bayyana irin karfin iko da suke dashi a birnin Mogadishu,inda suka fice daga zauren tattaunawa da suke gudanarwa da kungiyoyin musulmi masu sassaucin raayi.

Mataimakin ministan harkokin waje na kenya,Moses Wetangula ,ya fadawa taron manema labaru a birnin nairobi yau cewa,nanda yan makonni ayarin farko na dakarun hadin gwiwa daga kasashen gabashin Afrika zasu isa Somalia.To sai dai ya bayyana cewa sasantawa tsakananin kungiyoyin musulmin da gwamnatin rikon kwarya,nada matukar tasiri domin cimma nasarar tura dakarun.An cimma kudurin tura dakarun Afrikan zuwa somalia ne,a wajen taron hafsan hafsoshin sojin kasashen Kenya,da uganda da Habasha da Somalia da Eritria da Djibuti da Sudan,awanda ya gudana a birnin Nairobi ayau.