1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa ta juya wa Firaminista baya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 31, 2016

Majalisar dokokin Tunusiya ta kada kuri'ar nuna kin amincewa da Firaministan kasar Habib Essid da gaggarumin rinjaye.

https://p.dw.com/p/1JZCR
Firaministan Tunusiya Habib Essid da majalisar dokoki ta juya wa baya
Firaministan Tunusiya Habib Essid da majalisar dokoki ta juya wa bayaHoto: picture-alliance/dpa/EPA/Str

Rahotannin sun nunar da cewar 'yan majalisa 118 ne suka kada kuri'ar kin amincewa da shi uku kacal suka mara masa baya yayin da 27 suka kauracewa kada kuri'ar. Dama dai Firaminista Essid na fuskantar suka daga da yawa na 'yan siyasar kasar da ke zarginsa da gaza saita al'amura a kasar da ke Yankin Gabashin Afirka, wadda kuma ke fuskantar matsalar tabarbarewar tattalin arziki da rashin aikin yi ga matasa, kana kuma ta fusknaci hare-haren ta'addanci. A watan Yunin da ya gabata ne dai Shugaba Beji Caid Essebsi na Tunusiyan ya bukaci da a kafa gwamnatin hadin kan kasa. Tunusiya dai na zaman kasar da guguwar juyin-juya hali ta fara kadawa a shekara ta 2011 tare da yin awon gaba da gwamnatin Shugaba Zine El Abidine Ben Ali,kafin daga bisani guguwar ta bazu zuwa sauran kasashen Larabawa.