Tuntubar ′yan Takarar Majalisar Turai Ta Kan Internet | Siyasa | DW | 27.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tuntubar 'yan Takarar Majalisar Turai Ta Kan Internet

Tashar DW ta bude wani shafi na musamman domin ba wa jama'a wata kafa ta tuntubar 'yan takarar majalisar Turai na illahirin jam'iyyun siyasar Jamus, kai tsaye

Silvana Koch-Mehrin 'yar takarar FDP a majalisar Turai

Silvana Koch-Mehrin 'yar takarar FDP a majalisar Turai

‚Yar takara ta farko da wakilin DW ya halarci zaman mahawararta ta kan Internet a ofishinta dake Berlin ita ce Silvana Koch-Mehrin ‚yar jam’iyyar FDP, wacce aka sameta ta shagala da mayar da martani da kuma amsa tambayoyin da jama’a ke fuskantarta da su. Sai dai kuma ire-iren wannan tattaunawa ta kan Internet abu ne na gajeren lokaci kamar yadda jami’ar siyasar ta nunar, ko da yake akwai wasu tambayoyin, wadanda mutum ba zai iya amsa su a takaice ba. Tambayoyin dai suna kwararowa ne ba kakkautawa, a yayinda su kuma jami’an siyasar ke amsa su a cikin gaggawa. Da yawa daga cikin tambayoyin sun shafi batutuwa ne kamar kwasta, manufofin jin dadin rayuwar jama’a, karbar karin kasashe a Kungiyar Tarayyar Turai da dai makamantansu. A lokacin da yake bayani a game da fasahar gudanar da tattaunawar ta kan Internet a na’ura mai kwakwalwa Rick Spökel dake daya daga cikin masu alhakin wannan salo na musayar yawu cewa yayi:

Wadannan amsoshin ana tura su ne kai tsaye ba tare da an sake bitarsu ba. Dangane da tambayoyin kuwa, mai alhakin gabatar da shirin shi ne ke tantance su ya kuma rattaba su a jere bayan an tace su saboda gudun fuskantar jami’an siyasar da bakar magana daga bangaren masu aiko da tambayoyin.

Wannan sabon salo na musayar yawu wata babbar kalubala ce ga fitattun jami’an siyasa irinsu Silvana Koch-Mehrin. Domin kuwa mai yiwuwa, a kokarin ba da amsa a hargitse, a caba tabargaza. Wato dai lamarin daidai yake da hira ta rediyo ko telebijin, inda wajibi ne mutum yayi taka tsantsan da ire-iren kalaman dake fita daga bakinsa, domin gudun kuskure. Babbar manufar gabatar da wannan sabon salo na tattaunawa kuma shi ne domin ba wa masu amfani da na’ura mai kwakwalwa wata dama ta shiga a rika damawa da su tare da samun cikakkun bayanai a game da zaben majalisar Turai da kuma manufofin hadin kan Turai baki daya. Kawo yanzun sama da mutane dari suka yi amfani da wannan dama domin tuntubar ‚yan takarar neman wakilci a majalisar ta Turai kai tsaye domin jin ta bakinsu a game da ayyukan majalisar da kuma rawar da take takawa da kuma wacce zata iya takawa nan gaba a al’amuran nahiyar.