Farashin man fetur zai karu a Tunisiya
June 1, 2018Talla
Matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin kasar ta dauka tun bayan hambarar da shugabancin Zine El-Abidine Ben Ali a shekara ta 2011 na fuskantar bore daga babbar kungiyar kwadago ta kasar, wadanda suke korafin matsin tattalin arziki ya addabi al'umma musamman ma ma'aikata.
Cikin wannan makon ne tawagar wakilan Asusun bada Lamuni na Duniya wato IMF suka ziyarci kasar ta Tunisiya don ganawa da mahukuntan kasar.