1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya: An kafa dokar hana fitar dare

Ahmed SalisuJanuary 22, 2016

Hukumomi a Tunisiya sun sanya doka ta hana fita a fadin kasar sakamakon zanga-zanga da kuma bore da mutane ke yi saboda rashin aikin yi.

https://p.dw.com/p/1HiOc
Tunesien Proteste in Tunis
Hoto: Reuters/Z. Souissi

Ma'aikatar cikin gidan Tunisiya din ce ta bada sanarwar wannan doka ta hana fita wadda za ta yi aiki tsakanin karfe 8 na dare zuwa biyar na Asuba kuma za ta fara aiki ne daga yau Juma'a.

Mai'aikatar ta ce ta dau wannan matakin ne duba da irin hadarin da ke akwai na afkawa mutane da kuma dukiyoyinsu. To sai dai wani matashin ya ce dokar ba za ta hana su bore ba don a cewarsa ''gwamnati za ta sauraremu ne kadai in muka yi bore. Tun shekaru biyar da suka gabata muka mika mata bukatunmu amma har yanzu ba ta sauraremu ba.''