Tunawa da kulla zumuntar Jamus da Faransa
September 22, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaranta na Faransa Francois Holland sun gudanar da bikin tunawa da ranar da kasashen biyu sasanta da juna bayan yakin duniya na biyu. Shugaban Faransa Francois Holland ya yi tattaki zuwa birnin Ludwigsburg dake kudu maso gabashin Jamus domin haduwa da shugabar gwamnati Angela Merkel wajen gudanar da bikin zagayowar ranar ta sake kulla zumuntar kasashen biyu. A wannan wuri ne shekaru 50 da suka wuce tsohon shugaban Faransa Charles de Gaulle ya gabatar da jawabi ga matasa Jamusawa. An yabawa jawanin na Charles de Gaul a matsayin babban mataki na karfafa zumunta tsakanin Jamus da Faransa bayan da kasashen biyu suka gwabza fada a yakin duniya inda ma ake danganta su a matsayin manyan abokan gabar juna. Tsohon shugaban Faransar Charles de Gaul da takwaransa na Jamus na wancan lokaci Konrad Adenauer sune suka dabbaka yunkurin sasantawar kasashen biyu. Wannan yunkuri na kasashen biyu ne ya zama tambarin hadin kan nahiyar turai baki daya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi