1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100910 USA Islam 11.9.

Halimatu AbbasSeptember 10, 2010

Amirkawa na ci gaba da tafka muhawara akan harin 11/9.

https://p.dw.com/p/P9X2
Filin "Ground Zero"Hoto: AP

Har yau ana ci gaba da mahawara ba ƙaƙƙautawa a ƙasar Amirka dangane da hare-haren nan na sha ɗaya ga watan Satumban shekara ta 2001, abin da ya haɗa har da saɓanin da ake famar yi a game da barazanar ƙona Alƙur'ani mai girma da Pasto Terry Jones ya yi da kuma shirin musulmi na gina wani ƙasaitaccen masallaci a kurkusa da inda aka kai harin a birnin New York, misalin shekaru tara da suka wuce. A halin da ake ciki yanzu dai tuni shi kansa shugaban Amirka ya tsoma baki a lamarin ko da yake manazarta na saka ayar tambaya a game da ko shin kafofin yaɗa labarai na yayata batun ne sakamakon fafutukar 'yan siyasa ta neman goyan baya ko kuwa dai a haƙiƙa Amirkawa na ƙyamar musulunci ne.

Imam Feisal Abdul Rauf
Feisal Abdul Rauf, limanin a Amirka.Hoto: Creative Commons/shizhao

Kimanin kashi 66 daga cikin 100 na Amirkawan da aka tambayi albarkacin bakinsu ne suka bayyana adawarsu da shawarar gina wani masallaci a dandalin da aka kira wai "Ground Zero", inda aka kai hari akan tagwayen ginin nan na cibiyar ciniki ta duniya a New York ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001. Wani abin lura a nan shi ne akan wannan titin da ake batu game da shi akwai gidajen giya da ma na karuwai, amma wannan maganar ba ta damu ainihin mutanen da jaridar Washington Post ta binciki ra'ayinsu ba, saboda a ganinsu waɗannan gidajen ba su da wata alaƙa da 'yan ta'addan da suka ragargaza cibiyar cinikin ta duniya. 'Yan ta'addan suna amfani da sunan musulunci ne don cimma manufofinsu kawai. Tun dai bayan harin na 11 ga watan Satumba, wanda ya kaɗa zukatan Amirkawa da ma duniya baki ɗaya, Amirkawan kan damu da zarar sun yi tunani game da musulunci in ji Jim Kolbe, ƙwararren masani akan manufofin hijira a cibiyar bincike ta Marshall Fund da ke nan Jamus.

Ya ce:"Idan maganar ta shafi wasu mutane ne da suka san su sai ga ka ba wata matsala. Amma da zarar sun samu wasu rahotanni, waɗanda akan danganta su da musulunci a bisa kuskure, sai ka ga wasu daga cikinsu na bayyana ƙyama."

Bisa ga ra'ayin Kolbe dai Amirkawa ba su ƙyamar musulunci. To sai dai kuma kashi 49 daga cikin 100 na mutanen da aka binciki ra'ayinsu ba su da tunani na gari game da addinin. Amma hakan na da nasaba ne da salon rahotannin kafofin yaɗa labarai a cewar John Esposito darektan cibiyar nazarin al'amuran Larabawa da addinin musulunci a jami'ar Georgetown da ke birnin Washington.

Ya ce:"Tun shekaru da dama da suka wuce ake samun masu gabatar da shirye-shirye a tashoshin telebijin masu zaman kansu, galibi waɗanda ke da tsattsauran ra'ayin riƙau da ma jaridu da kuma wasu pastoci masu tsattsauran ra'ayi da ke yayata manufofin ƙyamar musulmi. Kuma al'umar Amirka na naƙaltar waɗannan rahotannin a kullu-yaumin."

NO FLASH Koran-verbrennung Koran Christen USA Islam
Rev. Terry Jones, mai son ƙonar al-Ƙur'ani mai tsaƙi.Hoto: AP

A baya ga haka akwai wasu jami'an siyasa da kan bayyana ƙyamar musulunci don neman ƙuri'u. A saboda haka ba abin mamaki ba ne kasancewar yau tsawon watanni biyu kenan ake fama da zazzafar mahawara akan cibiyar musulmin da ake da niyyar kafawa a birnin New York. John Esposito ya ƙara da cewar: "Bisa saɓanin yadda lamarin yake a Turai, musulmi a Amirka sun saje ana damawa da su a fannoni na tattalin arziƙi da ilimi da kuma siyasa. Yawa-yawancinsu na da albashi mai tsoka fiye da sauran takwarorinsu. A haƙiƙa ma dai Yahudawa ne kawai suka tsere musulmin a fannin ilimi mai zurfi a nan Amirka."

Sai dai kuma duk da wannan kyakkyawan matsayi musulmin na fama da wahala wajen wanke kashin kazan da aka shafa musu a ƙasar ta Amirka, musamman ma a halin da muke ciki yanzu inda tuni aka gabatar da yaƙin neman zaɓen 'yan majalisa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Halima Balaraba Abbas