1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru hudu da hadarin nukiliya a Japan

Suleiman BabayoMarch 11, 2015

Shekaru hudu kenan da faruwar hadarin makamashin nukiliya na Fukushima da ke kasar Japan, amma har kawo yanzu ana ci gaba da fuskantar matsaloli.

https://p.dw.com/p/1EolE
Girgizar kasar da ta yi sanadiyyar samun hadari a tsahar nukiliya ta Fukushima
Girgizar kasar da ta yi sanadiyyar samun hadari a tsahar nukiliya ta FukushimaHoto: picture alliance/dpa

Bala'in ya faru sakamakon girgizar kasa da aka samu wadda ta janyo ambaliyar ruwa. Sai dai tun bayan faruwar lamarin har zuwa yanzu wasu mazauna kauyuka suna rayuwa a matsugunai na wucin gadi, abin da magajin garin Futaba ya ce haka ya zama abin kunya ga kasar da take tunkaho da ci gaba. Anaiwa mutanen da suke rayuwa a matsugunan wucin gadin lakani da 'yan gudun hijiran nukiliya. Ichiro Takano na daya daga cikin wadanda ke zaune a sansanin 'yan gdudun hijirar duk da cewa ba gida ba ne, amma ya shafe shekaru hudu a wurin. A baya dai yana aikin gine-gine ne amma tun bayan faruwar lamarin ya zamo dan gudun hijira.

Shuru na minti daya Domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a Fukushima
Shuru na minti daya Domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a FukushimaHoto: Reuters/Y. Shino

Shekaru hudu ba tare da dangi ba

A sansanin an samar da wajen kiwon kifi, amma haka bai wadatar ba a cewar Ichiro Takano da ya kasance daya daga cikin ‚yan gudun hijiran nukiliya fiye da 125,000 wadanda tun a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2011 suka kasance suna rayuwa a kauyukan da ke kewaye da tashar nukiliya. Kauyen Futaba yanzu haka babu mai rayuwa a ciki duk al'umar garin suna sansanin 'yan gudun hijira na nukiliya wadanda kuma ke kokawa da yadda kudaden da gwamnati ta basu basu wadatar ba. Al'ummomi mazauna kauyuka da garuruwa 59 da suke kewaye da tashar nukiliya ta Fukushiman ne aka tayar bayan hadarin da aka samu a tashar.

Gwamnati ta gaza

Kazuo Sato dan shekaru 73 yana cikin wadanda aka tayar kuma ya bayyana cewa sun dawo daga rakiyar gwamnatin kasar ta Japan kasancewar shekaru hudu ke nan da afkuwar lamarin amma babu abin da aka yi musu. Shirou Izawa shi ne magajin garin na Futaba da ke da mazauna kimanin mutane 7000 kafin faruwar hadarin na tashar nukiliya da ya tilasta mayar da mazauna garin sansanin 'yan gudun hijiran nukiliya, ya koka ganin cewa a kasar da take tunkaho da wayewa ne al'uma ta shiga irin wannan hali yana mai cewa bisa tsari bai kamata mutane su zauna a sansanin wucin gadi na fiye da shekaru biyu ba. An yi shiru na minti daya, albarkacin cika shekaru hudu da faruwar girgizar kasa mai karfin maki 9 da ta janyo ambaliyar ruwan da dubban mutane suka hallaka, da kuma janyo hadarin nukiliyar na Fukushima.

Japan Gedenken an die Opfer der Erdbeben-, Tsunami- und Atomkatastrophe von 2011
Yin addu'oi ga wadanda hadarin Fukushima ya rutsa da suHoto: Reuters/Kyodo