1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da ambaliyar Tsunami

December 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvEx

A yau ake gudanar da adduoin tunawa da cikar shekara guda tun abkuwar balain ambaliyar ruwa ta tsunami,inda a yau sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya aike da sako ta hanyar bidiyo,zuwa ga iyalan wadanda suka halaka da wadanda sukayi hasarar dukiyoyinsu a lokacin ambaliyar a kudancin Asiya.

Kofi Annan yace,har yanzu da sauran aiki a gaba na sake farfado da yankin,kodayake yace an samu ci gaba awasu bagarorin,tunda yara yanzu sun koma bakin karatunsu,an kuma kare yaduwar annoba,dubban wadanda suka tsira kuma sun samu aikin yi,yana mai yabawa dukkan wadanda suka bada gudumowarsu a lokacin wannan balai.

Haka shima tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton,wanda kuma shine mai kula da aiyukan taimako na Majalisar dinkin duniya akan Tsunami ya yaba da yadda aka samu farfado da wasu yankuna da balain ya shafa,hakazalika ya yaba da taimako da aka samu kawo yanzu kodayake yace har yanzu ana bukatar karin taimako domin farfado da saurayn yankunan da abin ya shafa.

Ana ci gaba da aduoi a bangarori dabam dabam na Asiya domin tunawa da kimanin mutane dubu 220 da suka halaka cikin ambaliyar ta tsunami.