Rigingimu da hanyoyin warware su
November 3, 2015Talla
A shirinmu na Ji ka Karu mai illimantarwa da fadakarwa cikin nishadi, ranar laraba (04-11-2015) za mu kawo muku kashi na bakwai na shirinmu a kan rikice-rikice da hanyoyin warwaresu, mai suna bin sahun iyaye da kakanninmu. A wancan kashin, mun ji yadda zaman lafiya ya wanzu a Kwarin Guga bayan da aka yi wani shirin sulhu, to shin wannan sulhun zai dore? Ganin cewa akwai wani shirin bayan fagen da ake yi na kawo hargatsi a zaben da ake sa ran yi a Kwarin Gugan? Ku kasance da mu dan jin yadda za a kaya …