Tsuke bakin aljihun gwamnatin Birtaniya | Labarai | DW | 20.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsuke bakin aljihun gwamnatin Birtaniya

Ministan kuɗin Birtaniya ya bayyana matakan tsimi da tanadi domin riga kafi ga abkuwar matsalar tattalin arziki

default

Minisatan kuɗin Birtaniya George Osborne na bayyana matakan tsimi da tanadi

Ministan kuɗin Birtaniya George Osborne, ya bayyana wasu sabbin matakai na tsuke bakin aljihun gwamnati.

Fasalin da ministan ya gabatar, ya tanadi tsimin Euro miliyan kusan 100 a tsukin shekaru biyar masu zuwa. Wasu daga illolin wannan tsimi da tanadi sun haɗa da yin asara guraben aiki  500.000, da kuma ƙara harajin kayan masarufi.

A lokacin da ya yi bayani gaban ´yan majalisa Osborne ya ce da su:Za mu ɗauki lokaci mai yawa kafin mu biya ɗimbin bashin da mu ka yi gado. Amma zan tabbatar ma ku da cewar ,wannan kasafi da mu ka yi, zai taimaka mu gaggauta biyan bashin, har ma mu gina ƙarin asibitoci da makarantu.

Cemma a jiya, Firayim Ministan David Cameron, ya bayyana rage kashi takwas cikin ɗari, na  kasafin kuɗin ofinshin ministan tsaro a cikin shekaru biyar.

A sakamakon wannan shiri,sojoji dubu 20 na Birtaniya da ke jibge  a nan Jamus tun ƙarshen yaƙin duniya na biyu, za su koma gida kamin shekara ta 2020.

Wannan shiri na gwamnatin Birtaniya na da burin riga kafin faɗawa matsalar tattalin arziki.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal