1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsufar shaugabannin Afirka

March 26, 2010

Bunƙasar yawan matasa a ɓangare guda da tsofuwar shuagabannin Afirka a ɗaya ɓangaren na daga cikin abubuwan da jaridun Jamus suka duba

https://p.dw.com/p/MevJ
Shugaba Mugabe na Zimbabwe mai shekaru 86 da haifuwa yanzuHoto: AP

A yau dai zamu fara ne da duba rahoton jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce a ƙasar Sudan, a daidai lokacin da aski ya ƙarato gaban goshi dangane da zaɓen da aka shirya gudanarwa a cikin watan afrilu mai kamawa hali na ɗarɗar ya fara rutsawa da zukatan jama'a. Jaridar ta ce:

"A halin yanzu haka dai ana daɗa samun ƙarin yawan masu yin kiran ɗage wa'adin zaɓen da aka shirya gudanarwa a Sudan daga 11 zuwa 13 ga watan afrilun mai kamawa saboda tsoron munanan matakai na maguɗi a arewaci da kuma kudancin Sudan baki ɗaya, kuma kawo yanzun, ko da yake ƙasa da makonni uku ne ya rage kafin zaɓen amma har yanzu ba ta tantance ko wane ne ya cancanci shiga zaɓen ba, saboda hukumar zaɓen ƙasar ta yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kiraye da ake mata na gabatar da sunayen jam'iyyun 'yan takarar zaɓen."

Symbolbild Wahlen Sudan
Wa'adin zaɓe na daɗa ƙaratowa a ƙasar Sudan

Ita kuwa mujallar Der Spiegel dake fita mako-mako ta ba da la'akari ne da shugabanci a nahiyar Afirka inda take cewar:

"A yayinda a ɓangare guda nahiyar Afirka ke samun bunƙasar yawan matasa, amma a ɗaya ɓangaren shuagabannin nahiyar sai daɗa tsufa suke yi. A 'yan kwanakin da suka wuce ne shugaba Robert Mugabe na ƙasar Zimbabwe dake da shekarun haifuwa 86 ya ce bisa ga dukkan alamu zai sake tsayawa takarar zaɓe don wani sabon wa'adi na mulki. Shi kuwa Husni Mubarak na ƙasar Masar, wanda daga baya-bayan nan ne ya zo nan Jamus don neman magani ya sake wani sabon yunƙuri na fuskantar duk wata ƙalubala nan gaba duk da cewar a yanzu haka yana da shekaru 81 da haifuwa. Shugaba Gaddafi na Libiya mai shekaru 67 yau kimanin shekaru 41 ke nan yake mulki a Libiyan. Idan muka garzaya zuwa Liberiya zamu tarar da shugaba Johnson Sirleaf mai shekaru 71, sai Abdoulaye Wade a Senegal mai shekaru 83 da Kibaki na Kenya mai shekaru 78 na haifuwa. A lokacin da ƙasashen Afirka suka samu 'yancin kansu yawancin shuagabanninsu matasa ne dake da ƙwazo da himma da ra'ayoyi masu ma'ana game da makomar nahiyar. Amma a yanzu shuagabannin tsofaffi ne da ba abin da suka sa gaba sai tara abin duniya."

Präsident Abdoulaye Wade
Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal dake da shekaru 83 na haifuwaHoto: DW

A garin Timbuktu dake yankin hamadar ƙasar Mali, nahiyar Afirka ta fara sake lalubo tarihinta na rubuce-rubucen ajami. Jaridar Die Zeit ce ta rawaito wannan rahoton inda take cewar:

"Timbuktu dai tayi ɗaruruwan shekaru tana zaman cibiyar ciniki da ilimi. Daga nan ne kuma fasahar rubuce-rubuce da haruffan larabci ya yaɗu zuwa sauran sassa na Afirka. Rubuce-rubuce da aka fi saninsu da ajami kafin Turawa na Faransa da Birtaniya su shigo da nasu salon suna masu gusar da wanda al'umar Afirka ta gada tun daga kakannin-kaka. A yau akasarin matasa na Afirka ba su da wata masaniya a game da tarihin rubuce-rubuce a nahiyar. Binciken taskar dubban-dubatar litattafan dake jibge a Timbuktu shi ne kawai zai kawo ƙarshen watsin da ake yi da tarihin Afirka."

Kamele in Timbuktu Mali
Timbuktu tsofuwar cibiyar kasuwanci da ilimi a AfirkaHoto: picture-alliance/ dpa

A wani sabon ci gaba kuma wayar salula sai daɗa yaduwa take yi a nahiyar Afirka, a cewar jaridar Financial Times Deutschland, wadda wannan tamkar gobarar titi ce ga kamfanonin salula, inda mutane ke musu ciniki duk kuwa da cewar ba su da ajiyar ko sisin kwabo walau a banki ko a gida.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala