Tsoron wani yunkurin juyin mulki a Chadi | Labarai | DW | 22.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsoron wani yunkurin juyin mulki a Chadi

Sojoji dake neman a biya su albashinsu a kasar Chadi sun,sun yi harbe harbe a kusa da ofishin shugaban kasa,wanda ya sake tsorata jamaa game da sake wani yunkuri na juyin mulki a kasar.

Wani jamiin diplomasiya daya bada wannan bayani,yace,wannan harbi ya girgiza mazauna garin Njemmaina,wadanda suka fara tserewa daga gidajensu,da wuraren aikinsu,yayinda ake yada jita jitar wani yunkurin juyin mulki.

Tun farko a jiya,ministan yada labarai na Chadi,ya baiyana cewa shugaba Idris Derby yana gabashin kasar,inda yake baiwa soji umurni game da wasu yan tawaye da suke kokarin hambarar da shi tun watanni da suka shige.

Gwamnatin kasar ta Cadi a makon daya gabata tace yan tawaye suna kokarin kashe Idris Derby,wanda shima ya kwaci mulki a 1990.