1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohuwar P/M Benezir Bhutto ta koma gida Pakistan

October 18, 2007

Tohuwar Premiyan Pakistan Benezir Bhutto ta koma gida bayan gudun hijira na shekaru takwas

https://p.dw.com/p/BtuL
Dubban jamaá suka yi dafifi a birnin Karachi domin yiwa Benezir Bhutto marhaba
Dubban jamaá suka yi dafifi a birnin Karachi domin yiwa Benezir Bhutto marhabaHoto: AP

A ranar Alhamis ɗin nan ne tsohuwar P/M Pakistan Benezir Bhutto ta koma gida bayan tsawon shekaru takwas tana gudun hijira. Dubban jamaá suka yi dafifi a birnin Karachi domin yi mata lale marhabun. Tun shekaru da suka wuce Bhutto ta lashi takobin koma gida Pakistan domin kawo ƙarshen gwamnatin kama karya ta mulkin sojin a ƙasar.

Da take jawabi ga dubban magoya bayan ta, Benezir Bhutto wadda ke cike da hawaye da murna na shauƙin komawar ta gida, ta yi godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya bata damar ganin wannan rana, ta komawa ƙasar haihuwar ta. Tana mai cewa ta dawo domin jagorantar jamíyar ta Peoples Party ga mulkin dimokraɗiya a babban zaɓe mai zuwa na ƙasa baki ɗaya.

“Bhutto tace abin da muke yi shine ƙoƙarin haɗa kan mutane yan kishin ƙasa, mu haɗa ƙarfi wuri guda domin ciyar da ƙasar mu gaba bisa tafarki na dimokraɗiya. A saboda haka ni da janar Musharraf mun yi taruruka kan wannan manufa ta wanzuwar dimokraɗiya a Pakistan. Ina fata wannan ta kasance manufa ta kawo sauyi daga mulkin kama karya zuwa mulki na dimokraɗiya. Ko da yake dai a yanzu ba zaá yi hanzarin yanke hukunci ba.“

Benezir Bhutto ta kuma shaidawa manema labarai cewa taron gangamin da jamaá suka yi wata alamar nasara ce ga alúmar Pakistan. Wani ɗan jaridan Pakistan Zahid Hussain wanda ya ganewa idanun sa taron gangamin yayi bayani da cewa “ Yace babu shakka wannan babban taron gangami ne wanda baá tsammaci cewa cikin dan ƙanƙanin lokaci zaá iya haɗa kan dubban jamaá daga sassan ƙasar Pakistan su yi fitowar ɗango domin yiwa Benezir Bhutto maraba ba. Kuma babu shakka wannan ya nuna cewa har yanzu jamíyar ta, tana da tasiri a zukatan alúma, bugu da ƙari lamarin na nuni da cewa yaƙin neman zaɓe ya kankama a wannan ƙasa.

Yayin da a hannu guda kakakin gwamnati Muhammad Ali Durrani yake baiyana gangamin tarben da cewa ba wani abun azo a gani bane domin ya gaza da abin da Benezir Bhutto ta tsammaci zata gani, a nata ɓangaren, mai magana da yawun jamíyar alúma ta Peoples Party jamíyar da Benezir Bhutto ke yiwa jagoranci tace “jamíyar alúma ta Peoples Party, jamíya ce wadda ta yi fice wajen magance matsalolin ta cikin girma da arziki, tana kuma da juriya ga dukkan wasu ƙalubale da barazana. Tace an sha yiwa Benezir Bhutto barazana iri iri kama daga kan gwamnati ya zuwa yan koren ta, ko da gabanin saukar ta, sai da aka yi mata barazana, amma ta nuna cewa bata tsoron kowa sai Allah, kuma yana tare da ita. Saboda haka a yanzu sai mu maida hankalin mu ga ƙasaitaccen bikin da zamu yi nan gaba. Idan ka lura da kyau zaka ga cewa birnin Karachi ya cika ya batse ba masaka tsinke tamkar bai taɓa ƙasaita ba kamar haka.“