1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohuwar komandan sojin Amurka tace Rumsfeld ya bada umurnin azabta fursunonin Abu Ghraib.

November 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuaM

Wata tsohuwar komandan sojan Amurka ta baiyana cewa,sakataren tsaron Amurka mai barin gado Donald Rumsfeld shi ya bada umurnin azabtar da yan gidan fursunan Abu Ghraib a Iraqi.

Brigediya janar Janis Karpinski ta fadawa wata jarida a Spaniya cewa taga wasikar da sa hannun Rumsfeld wadda ta bada umurinin bin tsauraran hanyoyi kamar hana barci wajen tambyyoyi ga fursunonin.

Karpinski wadda ke kula da gidan yarin har zuwa 2004,tace wasu hanyoyin samun bayanai daga fursunonin sun hada da sanya su tsayawa na tsawon lokaci,ko saka sauti mai karfi.

A shekarar 2004 ne aka maida Karpinski gida jim kadan bayan baiyanar hotunan wulakanci na Abu Ghraib,inda daga bisani aka rage mata girma zuwa matsayin kanar.

A makon daya gabata ne Karpinski tace a shirye take ta bada shaida kann Rumsfeld,idan kara da kungiyoyin kare hakkin jamaa na Jamus suka shigar game da abubuwan da aka aikata a Abu Ghraib ya kai ga bincike.