1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Rhodesia ya rasu

November 21, 2007
https://p.dw.com/p/CPra

Tsohon shugaban Rhodesia Ian Smith ya rasu a ƙasar Afrika ta kudu yana mai shekaru 88 a duniya.A 1965 Smith ya jagoranci fararen fata su 250,000 inda suka aiyana `yancin daga ƙasar Burtaniya maimakon amincewa da shawarar miƙa mulki ga baƙaken fata masu rinjaye.Ian Smith ya kasance firaministan ƙasar har zuwa lokacinda yaƙin sunƙuru na ya tilsata masa amincewa da tsagaita buɗe wuta a 1979.

A shekarar da ta biyo baya a ka gudanar da zaɓe inda Rhodesia ta koma ƙasar Zimbabwe ta yanzu,a lokacin nan Robert Mugabe ya zama firaminista.Smith ya ci gaba da adawa da Mugabe har zuwa lokacinda aka soke kujerun majalisa da aka keɓewa fararen fata a 1987.