Tsohon shugaban Nicaragua Daniel Ortega na kan gaba a zaben kasar | Labarai | DW | 06.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Nicaragua Daniel Ortega na kan gaba a zaben kasar

Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben shugaban kasa da na ´yan majalisar dokoki da aka gudanar jiya a kasar Nicaragua. Masu sa ido a zabe na kungiyar kasashen Amirka da na KTT sun bayyana zaben da cewa ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma ba wata alama ta satar kuri´u. Sun yaba da yadda mutane suka fita kwansu da kwarkwatansu don kada kuri´a. Alkalumman da hukuma ta bayar sun nunnar da cewa kimanin kashi 70 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri´a sun sauke wannan nauyi dake kansu. An yi hasashen cewa tsohon shugaban gwamnatin juyin juya hali na kasar Daniel Ortega zai lashe zabe.