1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Ivory Coast ya koma gida daga gudun hijra

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 12, 2005

Daruruwan magoya bayan Henri Konan Bedie ne suka tarbi hambararren shugaban kasar Ivory Coast daga gudun hijira da ya yi na tsawon shekara daya zuwa kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/BvZm
Hoto: AP

Bedie ya isa Ivory Coast ne kwana daya bayan sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya cikin wata hira da gidan rediyon Faransa ya da kyar ne a iya gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Ivory Coast,saboda shugabannin siyasa da kuma sauran jamiyu sun gagara hada kai wajen ganin an shirya zaben yadda ya kamata.

Har ya zuwa yanzu ba wani shirin na azo a gani da akayi game da wannan zabe da aka shirya zaa yi a watan Oktoba mai zuwa.

A wani taron manema labarai bayan isowarsa,a hedkwatar jamiyarsa ta Democratic Party daya daga cikin jamiyun adawa na Ivory Coast,Bedie ya sake nanata kiran day an adawa suke yiwa shugaba Laurent Bagbo da ya sauka daga karagar mulkin kasar da zarar waadin mulkinsa ya cika a wata mai zuwa.

Henrie Konan Bedie,wanda akayiwa juyin mulki a shekarar 1999,bayan yayi mulki na tsawon shekaru shida,ya kuma yi zaman hijira na shekara guda a Faransa,yayi kira da a lakaba takunkumi akan wadanda suke hana ruwa gudu a shirin zaman lafiya na Ivory Coast da kuma wadanda aka kama da laifin take hakkin bil adama.

Yace baa dauki matakan bin tsarin yarjejeniya da aka cimmawa ba,saboda haka akwai bukatar mu gano wadanda suka kawo wannan cikas.

Magoya bayan Bedie dai sun bi shi suna kade kade suna masu ihun Bedie shugaban kasa,yayinda ya bar harabar hedkwatar jamiyar tasa cikin tsatsauran tsaro na jamian tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da na jamian tsaron kasar.

Wani mai goyon bayan Bedie,Alain yapo yace yayi farin ciki cewa Bedie ya komo gida saboda ya sake karabar ragamar mulkin kasar.

Duk da cewa jamiyarsa ta zabe shi dan takarar kujerar shugaban kasa,Bedie bai baiyana wasu shirye shiryensa na zabe ba,amma akwai alamun cewa komawarsa gida zai kara kwarin gwiwa gay an adawa ya kuma kara dagula halin siyasar kasa da dama ke cikin wani rikitaccen yanayi.

Ya zuwa yanzu dai yan tawaye da suka kwace arewacin kasar a yakin basasa na shekara ta 2002 da ya barke bayan wani yunkurin juyin mulki da ya ci tura da aka shirya akan Laurent Gbagbo,sun ki amincewa su ajiye makamansu,haka kuma dukkan bangarori suna ci gaba da rikici akan yadda zaa kaddamar da yarjejeniyar zaman lafiya.

Jamiyar adawa ta New Forces,ta bukaci Gbagbo ya sauka daga mulki domin bada damar zaben shugaban rikon kwarya da zai shirya zabe a nan gaba,amma Gbagbo ya ki amincewa da wanna shawarar yana mai cewa kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar kasancewa bisa karagar mulki har sai an rantsar da sabon shugaba.

Shugaban daya babbar jamiyar adawar PDR,Alhassan Dramane Wattara,wanda ya taba rike matsayin Prime Minista a Ivory Coast a shekarar 1990 har yanzu bai sanarda komawarsa gida ba,daga gudun hijira da yakeyi a kasar Faransa.

Ana ganin wanna zabe yana da muhimmanci ga kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar Ivory Coast da ta rabe tsakanin gwamnati da ke rike da kudancin kasar da kuma arewa dake hannun yan tawaye tun yunkurin juyin mulki day a ci tura a 2002.