1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Chile Pinochet ya rasu

December 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuYQ

Allah yaiwa tsohon shugaban kama karya na kasar Chile Augusto Pinochet rasuwa.

Tsohon shugaban na Chile ya rasu ne yana da shekaru 91 da haihuwa mako guda bayan samun bugun zuciya.

An dai kaishi asibitin ne mao guda bayan daurin talala da akayi masa bisa zarge zarge da suka shafi take hakkin bil adama a lokacin mulkinsa a 1973 zuwa 1990.

Pinochet ya kwaci mulki ne ya kuma zamo daya daga cikin manyan shugabnin kama karya a kudancin Amurka,inda akalla mutane 3,000 suka rasa rayukansu hannun yan sanda a lokacin mulkin nasa.

Augusto Pinochet ya shafe tsufabsa ne yana fuskantar zarge zarge na take hakkin bil adama da cin hanci da rashawa.