1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Amirka Gerald Ford ya rasu yana da shekaru 93

Tsohon shgaban Amirka Gerald Ford ya rasu a jihar California ya na da shekaru 93. Wata sanarwar da mai dakin sa Betty Ford ta bayar, ta tabbatar da mutuwar tsohon shugaban na Amirka. Ford dai shi ne shugaban kadai da ba´a taba zaba a mukamin shugaban kasa ba. An nada shi kan mukamin mataimakin shugaba Richard Nixon sannan ya dare kan mukamin shugaban Amirka a shekara ta 1973 bayan abin kunyar nan da ya tilasta Nixon yin murabus. Ya yi fama da cutar huhu wato nemoniya a watan janerun wannan shekara sannan an yi masa aikin tiyata a zuciya har sau biyu a cikin watan agusta.