Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu dan wariya PW Botha ya rasu | Labarai | DW | 01.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu dan wariya PW Botha ya rasu

Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Pieter Willem Botha ya rasu a gidansa dake yammacin jihar Cape yana mai shekaru 90 a duniya. Botha wanda ake yiwa lakabi da babban kada saboda tsauraran manufofinsa shi ya shugabanci ATK a karkashin mulkin tsiraru farar fata daga 1978 zuwa 1989. Ya bijirewa dukkan suka da tofin Allah tsine daga kasashen duniya musamman akan tsarin mulkin nuna wariyar launin fata. Bayan ya yi murabus Botha ya ci gaba da nuna taurin kai inda yaki bayyana gaban hukumar tsage gaskisa da sasantawa wadda ta zarge shi da take hakkin bil Adama.