1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Manafort zai yi zaman kurkuku

Mohammad Nasiru Awal LMJ
June 15, 2018

Tun a cikin watan Oktoban bara aka tuhume Manafort da laifin halatta kudin haramu da kaucewa biyan haraji da yi wa banki zamba cikin aminci.

https://p.dw.com/p/2zeMv
USA Paul Manafort
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Martin

An aike da tsohon manejan yakin neman zabe na shugaban Amirka Donald Trump, wato Paul Manafort zuwa gidan wakafi. Wata mai shari'a a kotun tarayya da ke birnin Washington ta yanke hukuncin cewa akwai barazana ta yaudara da rashin gaskiya tare da Manafort.

Masu shigar da kara na gwamnati suna zarginshi da zama barazana ga shaidu a tuhumar da ake masa.

Tun a cikin watan Oktoban bara aka tuhume Manafort da laifin halatta kudin haramu da kaucewa biyan haraji da yi wa banki zamba cikin aminci da kuma kin rajistar wasu aikace aikace da yi wa wata gwamnatin kasar waje.

Tun a lokacin ake masa daurin talala a gida. Kotun na kuma zargin Manafort da aikata wasu laifuka da ba a faiyace ba.