1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon kwamandan Kureshawan Bosniya ya rasu

Mohammad Nasiru Awal SB
November 29, 2017

Slobodan Praljak da aka gurfanar a gaban kotun duniya ya rasu bayan da ya sha guba a daidai lokacin da za a yanke masa hukunci.

https://p.dw.com/p/2oTLB
Niederlande Slobodan Praljak trinkt Gift im Gerichtssaal in Den Haag
Slobodan Praljak lokacin ya kurba wani abu da aka ce guba ce a zauren kotunHoto: Reuters/ICTY

An katse zaman sauraren hukuncin da kotun hukuntan manyan lafukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Hague za ta yanke wasu Kureshawan Bosniya bayan aukuwar wata ba zata.

Lauyan Slobodan Praljak, daya daga cikin wadanda suka gurfana gaban kotun ya ce bisa ga dukkan alamu Praljak din ya sha guba a daidai lokacin da alkalai za su tabbatar da hukuncin daurin shekaru 20 da aka yanke masa.

Shi dai Praljak mai shekaru 72 kuma tsohon kwamandan sojojin Kureshawan Bosniya ya yi ta ihu a zauren kotun yana cewa shi bai aikata wani laifi ba, kafin ya kurba wani abu daga wata karamar kwalaba.

Alkalan sun katse zaman kotun, sun kuma kira likita nan-take.

Da yawa daga cikin tsoffin firsinonin Musulmin Bosniya da ke bibiyar zaman kotun ta akwatunan telebijin sun kadu da abin da ya faru.

Edo Batlak tsohon firsina ne a Bosniya.

"Ban ji dadin abin da Praljak ya yi a kotun ba. Ba zan so in ga ya mutu sakamakon gubar da ya sha ba. An same shi da aikata laifi, ina kuma fata zai rayu domin ya fuskanci hukuncin laifin da ya aikata."