1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon jami'in leken asirin Amirka ya samu mafaka

July 6, 2013

Shugabannin kasashen Nicaragua da Venezuela sun bayyana shirin ba da mafaka ga Edward Snowden, tsohon jami'in leken asirin Amirka.

https://p.dw.com/p/1935C
Hoto: Inti Ocon/AFP/Getty Images

Shugaban Nicaragua, Daniel Ortega ya shaida wa gangamin mutane a kasarsa cewa, a shirye yake ya bai wa Snowden mafaka karkashin wani yanayi. Sannan Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro ya ce zai bai wa Snowden mafaka saboda dalilan jinkai da kare shi daga Amirka, wadda ke nemansa ruwa a jallo, saboda fadar gaskiya.

Shugabannin na kasashen Latin Amirka sun yi tir da matakin wasu kasashen Turai na hana jirgin saman Shugaban Boliviya, Eva Morales wucewa ta sararin samaniyarsu, bisa zargin cewa yana dauke da Snowden-amarin da ya tilasta masa saukan gaggawa a Austiriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas