1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halaka tsohon jagoran yaki a kasar Burundi

Yusuf BalaAugust 15, 2015

Wasu mahara ne da ba a tantance ba suka harbe Kanar Jean Bikomagu a cikin motarsa, a dai dai lokacin da yake daf da shiga gidansa.

https://p.dw.com/p/1GG7x
Burundi vor Parlamentswahlen
Dakarun soja a BurundiHoto: Getty Images/AFP/C. De Souza

Tsohon jagoran sojan kasar Burundi da aka fafata dasu a yakin basasar da kasar ta yi shekaru goma sha uku da suka gabata ya kwanta dama a wani kisan gilla da aka yi masa a ranar Asabar din nan, wani abu da ke nuna kara shiga yanayi na fargaba da kasar ke sake kutsawa da ka iya haifar da sabon yanayi na yakin basasa.

Kanar Jean Bikomagu fitacce cikin tsaffin dakarun sojan kasar da ke da rinjayen 'yan kabailar Tutsi, wasu mahara da ba a tantance ba sun harbe shi a cikin motarsa, a dai dai lokacin da yake daf da shiga gidansa a Kinindo wani lardi da ke kudancin birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar, kamar yadda wani mamba a iyalan sojan ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. A cewar majiyar dan bindiga ya bude wa tsohon sojan wuta sannan ya bace daga wurin inda ita ma 'yarsa da yake tare da ita ta samu munanan raunika.

Wannan kisa dai na zuwa ne kasa da makwanni biyu da kisan Janar Adolphe Nshimirimana da ke zama na kusa kuma mai bada shawara ga Shugaba Pierre Nkrunziza .